Sabuwar baraka a APC, “an maida mu saniyar ware” – Wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC

0

Idan ba a manta ba daya daga cikin musabbabin samun rabuwar kai da barakar farko da jam’iyyar PDP ta fara gamo dashi shine samun rabuwar kawunan ‘ya’yan jam’iyyar da gaba da ta shiga tsakanin su da musamman makusantar shugaban kasa a wancan lokaci wato Goodluck Jonathan.

Dalilin haka ya sa suka kirkiro wata kungiya da suka yi suna sabuwar PDP.

Wadanda suka jagoranci wannan kungiya kuwa sun hada da gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a wancan lokacin.

Akwai Danjuma Goje, Aliyu Wamakko, Babangida Aliyu, Rotimi Amaechi, Bukola Saraki, Rabiu Kwankwaso da sauran su.

An yi ta kai ruwa rana tsakanin su da sauran ‘yan PDP da ke tare da shugaba Jonathan a wancan lokaci inda daga baya duk suka rikide suka afka jam’iyyar APC. Duk da dai wasu daga cikin su babi su ba.

A yau Laraba ne wadannan mambobi na tsohuwar kungiyar sabuwar PDP ta rubuta wata shimfidaddiyar wasika ga shugaban jam’iyyar APC John Oyegun suna koka wa da yadda jam’iyyar tayi watsi da su tun bayan gudunmuwar da suka ba gamayya jam’iyyun aka kada Jonathan da jam’iyyar PDP a 2015.

Kungiyar ta ce sun ba jam’iyyar APC mako guda ta amsa ta ko kuma ta dau mataki.

Abubakar Kawu Baraje ne ya saka wa wannan takarda hannu tare da tsohon sakataren jam’iyyar PDP Olagunsoye Oyinlola.

Share.

game da Author