Rungumar Trump da Buhari ya yi bala’i ne, ba alheri ba ne -Kungiyar Dalibai Musulmi

0

Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya, ta bayyana tayin da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa Buhari dangane da batun kashe-kashe a Najeriya, cewa ba alheri ba ne, bala’i ne, kuma hakan zai kara raba kan Najeriya.

Shugaban Kungiyar na Jihar Lagos, Amir Saheed Ashafa, ya bayyana haka a cikin wata takardar da ya raba wa manema labarai jiya Litinin a Lagos.

Trump dai ya bayyana wa Buhari cewa kashe Kiristoci da ake yi a Najeriya ba abu ne da gwamnatin Amurka za ta lamunta da shi ba.

A kan haka ne sai Ashafa ya bayyana cewa wannan kalami na Trump tamkar wata gobara ce fa idan ba a yi taka-tsantsan ba.

Don haka ya kamata Najeriya ta bi a hankali, ta daina karkarwar neman gwanintar hulda da Amurka.

Shugaban na Kungiyar Dalibai ya kara da cewa furucin Trump ya nuna kiyayya ga Musulmi da Musulunci a Najeriya.

Ya ce furucin da Trump ya yi, bangaranci ne kuma nuna goyon baya ne ga Kiristoci su kadai, ba tare da yin la’akari da dimbin musulmai da ake kashewa a kasar nan ba.

Daga nan sai ya ce ya na mamakin shin ko Trump bai sai dimbin Musulmin da ake kashewa a kasar nan ba ne, kamar a Zamfara, a Maiduguri inda a cikin jami’a har a masallaci an kashe musulmi, a Yobe da sauran wurare da dama.

Daga nan sai ya kira ga Buhari da yi taka-tsantsan domin kada garin gyaran doron da kasar nan ta samu wajen ta’addanci, a zo a karya gadon-baya baki daya.

Da yawan jama’a dai tun a jiya wasu na murna da kuma ganin Buhari ya ciwo nasara a ziyarar da ya kai Amurka.

Sai dai kuma tuni wasu da dama na ganin cewa an kwafsa sosai, domin Buhari bai yi wa Trump gyara a bayanin sa na kashe Kiristoci da ya ce a daina ba.

Da yawa sun so Buhari ya nuna wa Trump cewa ba kiristoci ne kadai ake kashewa ba. Kuma musulmai sun fi kiristoci yin asara a wannan kashe kashe da ke faruwa.

Idan ba a manta ba, kiristocin jihar Taraba sun kashe Fulani kusan 700 a Mambilla, sannan kuma bayan harin baya-bayan nan da aka kashe kirstoci 17 a Benuwai, su ma kiristoci sun kai harin fansa inda suka kashe Musulmi sama da 20 kuma suka kona masallatai biyu.

Share.

game da Author