RIKICIN MAKIYAYA: Wadanda aka kashe a Zamfara sun zarce na jihohin Benuwai da Taraba gaba daya – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nanata bayanin da ya taba yi a baya cewa wadanda suka rasa rayukan su a fadan makiyaya da manoma a Zamfara, sun zarce na Benuwai da Taraba gaba daya.

“Masu zagin Fulani da kisa, sun san cewa Fulani kamar yadda muka san su, sanda kawai su ke yawo da ita idan su na yawo. Maganar fara yawo da bindigu kuma wani sabon abu ne wannan. Amma dai masu wannan zargi su sani cewa an dade ana rikici da Fulani da makiyaya, tun ma kafin a haife mu.

Don haka ba daidai ba ne a ce rikici ne kawai tsakanin Fulani da Tivi ko sauran kabilu, kamar a cikin Taraba. To Zamfara fa? A can an kashe jama’a fiye da wadanda aka kashe a Benuwai da Taraba gaba daya.

“Ya kamata jama’a su fahimci cewa ruruta rikici ake yi, idan ana cewa fada ne na addinanci ko kabilanci.” Inji Buhari.

Da ya koma batun ganawar sa ta sirri da shugaban Amurka Donald Trump kuwa, Buhari ya ce, “Ba mu kulla wata yarjejeniya ba, tattaunawa kawai muka yi a tsakanin mu. Na farko shi ne maganar da ya yi cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya, amma abin da ke faruwa a coci-coci ya na faruwa Kudu-maso-Gabas da kuma Arewa. Amma sai su ce wai Fulani makiyaya ne ke karkashe su.”

Share.

game da Author