RAMADAN: Zamfara za ta ciyar da marayu dubu 30

0

Gwamnatin Jihar Zamfara za ta raba taimako na kudi da tufafi ga marayu dubu 30 a fadin Jihar.

Sanarwar ta ce za a raba musu kudaden da tufafin ne daga cikin baitulmalin kudaden zakka da gwamnatin jihar ke tarawa a duk shekara.

Daraktan karba da raba Zakka na jihar, Ibrahim Tudu ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Litinin, a Gusau, babban birnin jihar Zmafara.

Ya ce za a ba su tallafin ne a matsayin zakka, domin albarkar watan azumi.

Ya ce za a tantance marayun ne a fadin masarautu 17 da jihar ke da su cikin kananan hukumomi 14 na jihar.

Daraktan ya ce, kamar yadda musulunci ya tanadar, sai yaron da uban sa ya mutu, shi ne ya fada cikin lissafin marayu.

Ya ce gwamna Yari ya kara yara 5,000 ne a wannan shekara, daga 25,000 da aka bai wa tallafin a shekarar 2017.

Share.

game da Author