PDP ta yi fatali da zaben Kaduna, ta zargi APC da rura fitintinu

0

Jam’iyyar PDP ta zargi APC da haddasa fitintinu a yayin zabukan shugabannin mazabun ta, wanda ta ce hakan alamomi ne da ke nuna cewa za su rikita Najeriya a kan neman mukaman siyasa.

PDP ta ce APC ta fito karara ta na ruruta fitintinun ko-a-ci-ko-a-mutu, abin da ta kira sabubban haddasa karya doka da oda a Najeriya.

Kakakin jam’iyyar PDP, Kola Olagbondiyan ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar bayan rikitta-riktar da ta dabaibaye zabukan shugabannin shiyya na jam’iyyar APC a fadin kasar nan.

An dai samu tashe-tashen hankula da suka hada da kashe-kashe, harbe-harbe har da soke-soke da wukake. A wurare da dama kuma an samu rahoton kone-kone.

Wasu jihohin da aka yi kashe-kashe sun hada da Lagos, Rivers, Delta da Gombe.

PDP ta ce tun da APC ta hau gwamnati jam’iyyar ke ta rura wutar fitintinu a harkokin da suka danganci zabe.

PDP ta yi fatali da zaben Kaduna

A wata sabuwa kuma, kakakin na PDP ya bayyana zaben kananan hukumomi da ya gudana a ranar Asabar a Jihar Kaduna da cewa harkalla ce, magudi ne tuburan, kuma abu ne da zai iya tunzura jama’a.

Ya ce gaba da cewa rahotannin da ke fitowa daga rumfunan zabe sun nuna yadda PDP ke samun nasara, ita kuwa APC ta ke shan kaye.

“Sakamakon zaben da ya rika fitowa hujja ce mai nuna irin farin-jini da ‘jam iyyar PDP ke da shi a jihar. Don haka jam’iyyar PDP ba ta amince da harkallar da hukumar zaben jihar Kaduna ta yi ba, inda ta baddala sakamakon zabe, ta maida nasara akan APC.

“Mu na da hujjoji a wurare da dama inda aka dauke jami’an zabe, aka boye su wasu wurare, kuma duk aikin ejan din gwamnatin jihar Kaduna ne da taimakon jami’an tsaro. Alhali a lokaci daya kuma aka rika bayyana sakamako na bogi.”

Ya bada misali da abin kunyar da ya ce ya faru a Karamar Hukumar Kajuru, inda ya ce yayin da masu zabe da ejan-ejan ke zaman sauraron komawar jami’in zabe a sakateriyar karamar hukumar, inda aka sakamako ya nuna PDP ta cinye mazabu 9 daga cikin 10 da ke da su. Sai kuma can a Radiyon Nagarta aka rika bada sanarwar APC ce ta lashe zaben.

A kan haka ne PDP ta ce zaben na Kaduna fashi ne da rana tsaka, kuma jam’iyyar na kira ga shugaban zaben ta Kaduna, Saratu Bako da ta gaggauta soke sakamakon zaben, domin PDP ta ga duk abin da aka tabka a fadin jihar da sunan wai zabe.

Share.

game da Author