Olisa Metuh ya yanke jiki ya fadi a kotu

0

Tsohon Kakakin Yada Labaran Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, ya yanke jiki ya fadi a kotun.

Metuh ya fadi ne a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, yayin da ake ci gaba da shari’ar tuhumar sa da karbar naira miliyan 400 daga hannun Sambo Dasuki.

Dama kuma an dade ana kai shi a cikin motar daukar marasa lafiya kuma a kan gadon daukar majinyaci daga asibiti.

Ba a dade da shigo da shi cikin kotun ba, sai kotu ta nemi ya gabata a gaban mai shari’a.

Ya na cikin tafiya ne kafin ya karasa, sai ya yanke jiki ya fadi, abin da ya janyo kotun ta hargitse kenan.

An ce Metuh na fama da ciwon lakar kwakwalwa ne.

Duk kokarin da aka yi domin a bar shi ya fita waje neman magani, bai samu amincewa daga mai shari’a Okon Abang ba.

Lauyan Metuh, Emeka Etiaba, ya shaida wa kotu cewa shi zai cire hannun sa akan shari’ar, amma alkali ya ce kada ya yi haka nan.

Share.

game da Author