Obasanjo ya zabi Jam’iyyar da zai shiga

0

Kungiyar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ‘CNM’ ta zabi ta hade da jamiiyyar ADC domin gogayya da sauran jam’iyyu a zabuka masu zuwa.

Idan ba a manta ba an Kaddamar da sabuwar Kungiyar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa mai suna ‘Coalition for Nigeria’ ranar 31 ga watan Janairu a dakin taro na gidan Shehu Musa ‘YarAdua’, Abuja bayan kunne da ya ja wa shugaban Buhari da kada ya nemi tsayawa takara a 2019.

Tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola ya ke shugaban kungiyar.

Gwamnoni 10 da tsoffin da ‘yan siyasar kasar nan duk sun nuna goyon bayan su.

Share.

game da Author