NAFDAC ta dakatar da ayyukan wasu kamfanonin sarrafa magani uku a Najeriya

0

Kamfanonin sarrafa magani da hukumar NAFDAC din ta dakatar, sun hada da kamfani ‘Emzor Pharmceuticals Ind.Ltd’ dake rukunin gidaje na Ajoa jihar Legas, ‘Peace Standard Pharmaceutical Limited’ a Ilorin jihar Kwara da ‘Bioraj Pharmaceutical Limited’ shima a Ilorin jihar Kwara.

Jami’ar hukumar Mojisola Adeyeye wacce ta sanar da haka ranar Talata ta bayyana cewa sun rufe wadannan kamfanoni ne ranar 2 ga watan Mayu bayan an gano suna da alaka da sarrafa maganin ‘Codein’ da aka hana siyar wa a kasar nan.

” Bayan haka mun kuma rufe wadannan kamfanoni ne saboda rashin bada wasu mahimman takardu da bayanai a lokacin da muka ziyarci kamfanonin domin gudanar da binciken mu.”

Adeyeye ta kuma kara da cewa hukumar NAFDAC za ta bude wadannan kamfanoni ne idan kamfanonin sun bada hadin kai sun gabatar da wadannan takardu da bayanan da hukumar ke bukata.

Share.

game da Author