Muna zaman lafiya da Adam Zango sumul-mul – Ado Gwanja

0

Fitaccen dan wasan barkwancin nan kuma shahararren mawaki Ado Gwanja, ya karyata rade-radin da ake ta yadawa cewa wai basa ga maciji da Jarumi Adam Zango.

A hira da yayi da PREMIUM TIMES, Gwanja ya bayyana cewa duk wannan batu karya ne. Y ace suna nan tare da Adam Zango lafiya sumul.

“ Kasan ba a rasa wadanda basu rasa abin cewa a kullum. Su bi wurare suna fetsa maganganu iri-iri. Amma ni dai a sani na babu abin da ya shiga tsakani na da Adam Zango. Hasali ma shi maigida na ne domin ni a yaron sa na fara sana’a ta kuma har yan zu ma haka ne.

Bayan haka Ado Gwanja ya tabbatar mana cewa ya daina fitowa a fina-final da zai nuna shi a adan daudu.

“A’a yanzu kam na dai na fitowa a fina-finan da zai haska ni a matsayin dan daudu. Zan tsaya a barkwanci na kawai.

Game da wakoki kuma Gwanja ya gode wa masoyan sa sannan yayi musu albishir cewa zai ci gaba da kida musu wakoki masu dadi don nishadin su.

“Babu abin da zai ce wa masoya na sai godiya. Wakoki na sun karbu kuma zan ci gaba da yin su domin masoya na a ko-ina a kasar nan.

Gwanja ya shaida mana cewa yana shirin auracewa nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author