Kungiyar dake tallafawa masu fama da cutar kanjama na kasar Amurka (PEPFAR) ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike don sanin sahihin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau a Najeriya.
Jami’in kungiyar Mahesh Swaminathan ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai kan mahimmanci gudanar da wannan bincike a Najeriya.
Ya ce za a fara wannan aiki ne daga watan Yunin 2018.
” Za ayi wannan bincike da kididdiga a dukka jihohin kasar nan sannan zai dauke mu wata 6 muna yi. Wannan aiki zai taimaka wa kungiyoyi irin namu da gwamnatin Najeriya wurin shirya manofufi da hanyoyin da zai taimaka wajen kawo karshen yaduwar wannan cuta.
‘‘Sanin kowane cewa kungiyar mu ta kashe dala biliyan 4.7 a cikin shekaru 14 don kawar da cutar kanjamau a Najeriya sannan duk kokarin da gwamnatin kasar ke yi a wannan fanni cutar sai kara yaduwa yake ta yi.”
Kungiyar ta ce ba kanjamau ba har da wasu cututtukan.
A karshe shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau (NACA) Sani Aliyu, ministan kiwon lafiya Isaac Adewole da jami’in UNAIDS Erasmus Morah, duk yaba wa wannan kungiya bisa kokari da suke yi a kasar nan suna masu cewa hakan zai taimakawa Najeriyata samar da wasu dabarun da zai kawo karshen yaduwar cutar ganin cewa kasar bata da ainihin yawan lambar mutanen dake dauke da cutar a kasar.
Discussion about this post