Muhimman abubuwa 7 game da ciwon siga

0

Cutar siga ‘Diabetes’ da a ke kira ciwon siga ya kasu rabu kashi dabam dabam amma bayanai sun nuna cewa an fi kamuwa da wanda ake kira ‘Type -2 diabetes’.

” Kiba, shan taba, shan giya, yawan, shan kayan zaki, rashin motsa jiki da makamantan su na daga cikin abubuwa da ke sa a kamu da wannan cuta.

Masana wannan cuta sun bayyana cewa a dalilin kamuwa da ita mutum kan iya makancewa, kamuwa da cutar koda, shanyewar bangaren jiki hawan jini da sauran su.

” Bincike ya nuna cewa a shekarar 2015 cutar ta yi ajalin mutane sama da miliyan 1.6 a duniya.”

Abubuwan da za a kiyaye :

1. Ana iya cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Carbohydrates’ amma kadan domin samun karfi a jika.

2. A guje wa shan zaki. Ya kan yi wa mutane illar da kan iya yin ajalin mutum..

3. A maida himma wajen motsa jiki sosai. Hakan na taimakawa wajen samun lafiya.

4. Taba sigari, shan giya duk suna zama illa ga jikin mutum sannan suna yin sanadin kamuwa da wannan ciwo.

5. Mai dauke da cutar zai iya cin abinci kamar su kubewa (danya ko busasa) acca, wake, shinkafan da ake kira ‘Brown rice’ da sauran su.

6. A guji cin kayan lambu da daddare kamar su kankana da abarba domin suna tadan cutar a jikin mutum.

Share.

game da Author