Ministan Ma’adinai, Fayemi ya ajiye aiki

0

Ministan ma’adinai kuma dan takarar gwamnan jihar Ekiti, Koyode Fayemi ya sauka daga kujerar ministan ma’adinai na Najeriya yau.

Fayemi dai shine zababben dan takarar gwamnan jihar Ekiti a zaben gwamnan da za ayi ranar 14 ga watan Yuli.

Duk da cewa an sami rudanin gaske a zaben dan takarar jam’iyyar APC inda tsohon gwamna Segun Oni, ya kalubalanci zaben fidda dan takarar cewa an nuna son kai, yanzu dai kowa ya wasa takobin sa tsakanin dan takarar Fayose gwamna mai ci na jam’iyyar PDP da Fayemi na APC.

Shugaba Buhari ya hori jagorar jam’iyyar Bola Tinubu da saurarn jiga-jigan jam’iyyar a yankin Kudu maso Yamma da tabbata APC ce ta lashe wannan zabe na gwamna.

Shi ko gwamna Ayo Fayose cewa yayi yananan zai ga wanda zai doke dan takarar saa wannan zabe.

Share.

game da Author