An gurfanar da wani mutum mai suna Bawa Joshua a Kotun Majistare ta Ado-Ekiti, a bisa zargin sa da laifin lafta wa matar sa Grace, talgen tuwon semovita.
Jami’in dan sanda mai gabatar da kara, Johnson Okunade, ya shaida wa kotu cewa Joshua ya watsa wa Grace matar sa talgen ne ranar 7 Ga Mayu, 2018.
Ya ce wanda ake karar sun yi tankiya da matar ta sa ne, shi kuma ya fizgi tukunyar tuwo, ya sheka mata tafasassshen talge har ya lahanta ta.
Sai dai kuma lauyan wanda ake kara, mai suna Kayode Oyeyemi, ya roki kotu ta ba shi belin Joshua, kuma ya yi alkawari zai kawo shi kotu a duk ranar da ake son ganin sa.
Alkali ya bada belin sa a kan kudi naira dubu 50,000, da kuwa wanda zai tsaya masa.
An daga kara zuwa ranar 15 Ga Yuni, 2018.
Sai dai kuma wanda ake kara ya ce bai aikata laifin da ake tuhumar sa da shi ba.
Discussion about this post