Mashawarcin Buhari, tsohon gwamna da da wasu 25 sun nemi a rushe kwamitin Al-Makura

0

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Shegun Oni, Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC 25 na jihar Ekiti sun nemi a rushe duk wani aikin zaben da Kwamitin Gwamnan Jihar Nasarawa Tanko Al-Makura ya gudanar a zaben fidda-gwani na ‘yan takarar gwamnan jihar.

A watan Yuli mai kamawa ne dai INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihar ta Ekiti.

Baya ga wannan, sun kuma yi kira da a soke dukkan kuri’un da kwamitin ya tattara ya ce su ne aka kada a wurin zabukan, wanda ya karke da hatsaniya a fadin jihar.

Sun cimma yarjejeniyar nuna wannan korafi na su bayan da suka tashi daga wani taron gaggawa da suka gudanar a jiya Lahadi, a Ado Ekiti.

Wadanda suka ce ba su yarda da zabukan fidda-gwanin ba, sun hada da tsohon gwamna Segun Oni, Mashawarcin Buhari a kan harkokin siyasa, Babafemi Ujudu, tsohon Sanata Ayo Arise da Gbenga Aluko, Mojisola Yahaya, Bimbo Daramola da sauran su da dama.

Sai da Ministan Karafa da Ma’adinai, Fayemi, bai je wurin taron ba. Dama kuma gungun masu korafin sun yi zargi ne cewa an kwamitin Al-Makura ya tafka cuwa-cuwar kagaggen sakamakon zabe ne don a biya wa Fayemi din bukatar sa ta tsayawa takarar gwamna.

Fayemi, wanda shi ne gwamnan da Fayose ya kayar, a yanzu shi ne a sahun gaban sake neman kujerar, amma a wannan karo, a karkashin jam’iyyar APC.

Akwai da dama masu neman takarar da suka hada Oni da Ujudu da wasu da dama.

Fayemi ya tsaya kai da fata cewa ya na kan gaba wajen kirga kuri’a, don haka sakamakon sauran kananan hukumomi hudu tilas ya tsaya yadda ya ke.

Sauran ‘yan takara kuwa sun tsaya kai da fata cewa zaben duk an yi magudi, wanda abin kunya ne a ce jam’iyya kamar APC mai da’awar yaki da magudin zabe ta tafka wannan rashin adalci.

Sun ce dukkan rigingimun da suka faru, sun afku ne dalilin rashin adalcin da kwamitin shirya zabe na Gwamna Al-Makura ya tafka.

Yaya-Kolade ne ya karanta takardar bayan taron wadda sauran ‘yan takarar 27 suka amince kuma sa mata hannu. Kuma tuni sunn jaddada rashin yardarm su da zaben.

Share.

game da Author