Madrid ta zama zakaran kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai a karo na uku a jere

0

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kafa tarihin da zai yi wuya a iya karya shi a tarihin wasan kwallon kafa a nahiyar turai, ranar Asabar.

Madrid ta doke kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ci 3-1 a wasan cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar turai.

Dan wasan ta Gareth Bale ne dan wasa na farko da ya taba cin kwallo biyu a wasan karshe bayan an sako shi daga dawowa daga hutun rabin lokaci.

Shi kuwa Mohammed Salah da ake ganin zai nuna gwanintar sa a wasan ganin yadda ya yi fice a shekarar kwallon kafa na 2017/2018, in da yafi kowa cin kwallaye a kungiyar sa ta Liverpool da tarihin da ya kafa a tarihin kwallon kafa a kasar Ingila ya fice ne daga wasan bayan minti 30 da fara ta.

Mai tsaron bayan Madrid Sergio Ramos ne yayi masa durmushewar kura taga akuya in da nan take ya gulde a kafadar sa.

Ko kati katin gargadi ba a bashi ba.

Madrid ce kwallon kafa ta farko da ta ci wannan kofi sau uku a jere.

Mohammed Salah

Share.

game da Author