MADRID DA LIVERPOOL: Maimaita ‘Haduwar Iliya da Wargaji’ a Birnin Kiev

0

A gobe Asabar ne za a goge raini tsakanin Real Madrid da Liverpool domin fidda zakaran kulub din kungiyoyin kwallon kafa na Turai, na kakar 2018.

Za a yi wasan ne a shahararren filin wasan Kiev, daya daga cikin biranen kasar Rasha.

Birnin Kiev, shi ne wanda Hausawa suka fi sani da Birnin Kib, da ke cikin Littafin ILIYA DAN MAIKARFI, inda aka bada labarin kafsawar Iliya da Gogaji da kuma Wargaji, manyan dodanni biyu da suka hana duniya sakat tsoro a lokacin.

Wannan kafsawa da za a yi gobe Asabar ta tuna min labarin haduwar babban gwarzon mayaki, kuma barde, mai suna Iliya Dan Maikarfi da gawurtaccen dodo, Wargaji dan dodo Gogaji.

A karshe dai a Birnin Kiev Iliya ya kashe Wargaji, bayan kafin nan ya kashe baban na sa Gogaji.

Ana sa ran kafsawa tsakanin Madrid da Liverpool za ta kayatar sosai, fiye da wasu wasannin kwallo da suka gabata a cikin shekaru uku da suka gabata.

ABIN LURA:

Gaba dayan ‘yan wasan Liverpool babu wanda ya taba buga wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai da za a yi gobe. Babu wanda ya taba kaiwa ga wasan karshe ko da a wata kungiya ballantana a Liverpool.

Kusan dukkan ‘yan wasan Real Madrid sun buga wasan karshe a 2014, 2016 da 2017.

Gobe Real Madrid za ta buga wasan karshe shekaru uku a jere.

Rabon da wani kulub ya buga wasan karshe a jere, tun Juventus ta birnin Turin na Italy, inda ta kai har wasan karshe a shekarun 1996, 1997 da 1998.

A wannan ne karo na biyu da Madrid da Liverpool za su kafsa a wasan karshe.

Wannan ne karo na biyu da mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp zai kai wasan karshe.

Ya kai wasan karshe a shekarar 2013, amma Beryern Munich ta doke kulub din sa na lokacin, Borussia Dortmund a babban filin wasan kasar Ingila, Wembley , a ranar 25 Ga Mayu, 2013.

Tun da Zinadine Zidane ya fara koyar da Madrid a cikin Janairu, 2016, har yau ba a taba yin nasara a wasan siri-daya-kwale ba kan Madrid.

Madrid ta ci kofin sau 12, kuma sau 15 ta na zuwa wasan karshe. Sau uku kenan ta taba yin rashin nasar a wasan karshe.

Wasannin karshe shida da Madrid ta yi, duk ita ce ke yin nasara.

Wannan ne wasan karshe na 8 da Liverpool za ta buga. Ta ci kofi sau biyar, ta yi rashin nasara sau biyu a wasan karshe.

Nasarar Liverpool ta karshe, ita ce a shekarar 2005, kan kungiyar A.C Milan ta Italy.

Cristiano Ronaldo na Madrid ne akan gaba wajen yawan cin kwallaye a wannan gasa ta bana. Kuma ya fi kowane dan wasa na duniya cin kwallaye a gasar a tarihin gasar.

Mohammed Sala na Liverpool ne biye da shi a yawan cin kwallaye a wannan gasa ta 2018.

Dukkanin su biyu su na da gwaninta, nasibi da kuma sa’ar cin kwallaye.

Real Madrid ta fi Liverpool gogewa a gasar Zakarun Kwallon Turai.

Liverpool kuma ta na da ‘yan wasan da suka nuna wa duniya cewa, ‘na kawo karfi ya fi an grime ni.’

Shin ko Iliya Dan Maikarfi (Liverpool), zai iya kashe Real Madrid (Wargaji) a Birnin Kib, kamar yadda ta faru a cikin littafi, inda Iliya ya kamo dodo Wargaji, ya kai shi kofar fadar Sarkin Birnin Kiev ya kashe?

Share.

game da Author