Shugaban hukumar kula da kiwon lafiya na babban birnin tarayya Abuja Humphrey Okoroukwu ya karyata bullowar cutar kwalera kamar yadda wasu gidajen jaridu suka yayyada.
Okoroukwu ya fadi haka ne ranar Lahadi da yake zanta wa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya. Sanannan ya kara da cewa babu gaskiya a cikin wannan magana, jita- jita ce kawai ake ta yadawa.
Ya bayyana cewa wata irin ciwon ciki ne wanda ake kira ‘Gastroenteritis’ ta kama wasu mutane uku dake zama a Masilasi Jabi a Abuja sannan a yanzu haka sun fara samun sauki a asibiti.
A karshe ya yi kira ga gidajen yada labarai da su dunga samun sahihancin labaran su kafi yada don guje wa irin haka.
Sannan ya yi kira ga mazauna garin Abuja musamman na yanki Jabi da su tsaftace muhallinsu,ruwan sha da abinci don guje wa kamuwa da ciwon kwalera da ‘Gastroenteritis’.
Discussion about this post