Jami’ar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar za ta aika da ma’aikatan kiwon lafiya 39 zuwa kananan hukumomin Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu domin taimakawa mutanen kananan hukumomin dake fama da barkewar cutar kwalara a jihar Adamawa.
Bayan haka kuma ma’aikatan da za a aika wadannan kananan hukumomi zasu wayar wa mutanen garuruwan kai kan irin abubuwan da za su na rika yi domin kauce wa kamuwa da wannan cuta da kuma hanyoyin da zasu bi don dakile yaduwar wannan cuta.
Idan ba a manta ba, jami’in yada labarai na ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Adamawa Abubakar Muhammed ya bayyana cewa tsakanin kananan hukumomin Mubi ta kudu da Mubi ta Arewa jihar ana samun karuwar mutanen da ke kamu da cutar Kwalara.
Muhammed yace a yanzu haka mutane 434 sun kamu da cutar sannan ta yi ajalin mutane 13 a jihar.
” A Mubi ta Kudu mutane 223 sun kamu da cutar sannan mutane 6 sun rasu, a Mubi ta Arewa kuma mutane 211 ne suka kamu da cutar sannan 7 sun rasa rayukan su.”
A karshe jami’in babbar asibitin Mubi Ezra Sakawa ya ce mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar an sallame su.
Discussion about this post