Kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta MURIC, ta yi tir da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN dangane da zuguguta kisan Kiristoci da CAN din ke nuna ana yi, inda har ta shiga zanga-zanga a kan titina da cikin coci-coci.
MURIC ta ce kashe-kashen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma fa ya shafi kowa ba kiristoci kadai ba, kuma ba fada ba ne tsakanin musulmi da kirista.
Daraktan Kungiyar MURIC, Ishaq Akintola, ya kara da cewa duk da dai shi ma ya damu da matsalolin da kiristocin ke fama da ita, musamman a yankin ‘Middle Belt’, to ya kamata kuma ita kungiyar CAN ta fahimci cewa fa su ma Musulmi da dama fiye ma da kiristocin su na cikin irin wannan tsaka-mai-wuya.
Ya kuma kara bada misali da yadda ake kashe dimbin rayukan musulmi a fadan Boko Haram a Arewa-maso-Gabas, inda musulmi din ne ma ke da rinjaye.
Ya ci gaba da buga masa misali da irin yadda ake kashe musulmi a kowace rana a garuruwa da dazuka daban-daban na kasar nan.
Har ma ya buga wa CAN Misali da musulman da aka kashe wadanda kiristoci ne suka kashe su a Benuwai, a lokacin da ake tafiya rufe gawar kiristocin da aka kashe a Benuwai din.
“To abin tambaya a nan shi ne, don me su kuma Kiristoci za su kashe musulmai wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda matafiya ne ma su ba ‘yan cikin jihar Benuwai din ba ne?
Ya ce me ya sa kuma za su fito har su na da bakin magana a yanzu bayan sun yi kisan ramuwar gayya kuma.
Daga nan sai ya ce shi a ganin sa maimakon Kiristoci su ware can gefe su na wata zanga-zanga su kadai, to kamata ya yi su nemi a hadu kiristoci da musulmai a yi zanga-zanga bai daya, tunda ko wadanne na yin asarar rayuka a wannan kashe-kashe da ke addabar kasar nan.
“To wai ma in banda rashin kunya, me ya sa can a baya lokacin da ake kashe-kashe a lokacin mulkin Jonathan ba su yi masa zanga-zanga ba ne?
“Ko don yanzu musulmi ne ke mulki ba Kirista ba? Ko ba a kashe kiristoci ba a lokacin Jonathan ne? Ko kuwa kawai so suke yi su kifar da gwamnatin Buhari ne?”
Idan za a iya tunawa, a lokacin mulkin Jonathan, Boko Haram sun sace daliban Chibok mata sama da 250, wadanda akasarin su duk Kiristoci ne, amma Kiristoci ba su fito sun yi wa Jonathan zanga-zangar kasawa ko nuna talasuranci wajen kare lafiya da rayukan su ba.
Discussion about this post