Kungiya ta koka da kashe-kashen kabilanci a jihar Nasarawa

0

Tashe-tashen hankula da ke faruwa tsakanin kabilu mabambanta ya haifar da kashe-kashe a jihar Nasarawa.

Wata kungiyar ci gaba Egbura ce ta yi wannan kukan ganin yadda rashin jituwa ke kara muni tsakanin kabilar Egbura da Bassa a jihohin Kogi da Nasarawa.

Kwanan nan an dakile wani mummunan harin da aka nufi kaiwa jama’ar garin Umaisha da ke cikin jihar Nasarawa.

Shugaba da Sakataren kungiyar, Ibrahim Aguye da Yusuf Aboki, sun bayyana kisan a matsayin kisan-kiyashi kan kabilar Egbura.

Kabilun biyu, Egbura da Bassa sun fi yawa ne a kananan hukumomun Toto cikin jihar Nasarawa da Kuma Karamar Hukumar Bassa da ke cikin jihar Kogi.

Sun tunatar da cewa Kakakin Yada Labaran rundunar sojoji ya yi bayani kwanan baya da ya ce sojoji sun kama wasu mahara, wadanda aka tabbatar da cewa maharan daga cikin karamar hukumar Bassa suka tsaklako.

Sun ce an kuma kai hari a kauyukan Ugya, Kolo, Katakpa da Ogba da sauran kauyukan kabilun Egbura da dama kuma an kashe jama’a da yawa.

Har ila yau kuma kungiyar ta yi zargin cewa kashe-kashen ya na da alaka da siyasa, musamman ganin yadda aka tunkari zaben 2019.

Daga nan sai suka yi kira ga Hukumar Agajin Gaggawa, NEMA ta kai dauki a kauyukan Nasarawa da suka hada da: Nasarawa Egbura indigenes from Kolo, Kuwa, Kokoto, Kanyehu, Dausu, Ogba, Ugya, Katakpa, wadanda a halin yanzu su ka zaman gudun hijira a cikin garin Umaisha da kewaye.

Sun kuma yi kira ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ya gaggauta maida al’ummar Egbura mazauna kauyukan Ogbonka, Ogbaozanyi, Ozugbe, Ahutara, Okanga da Ibiroko Egbura cikin karamar hukumar Bassa ta jihar Kogi, wadanda ke neman mafakar hijira a cikin jiahar Kogi.

Share.

game da Author