Ko a kara mana albashi ko mu ki zaben mutum a 2019 -Kungiyoyin Kwadago

0

Gamayyar Kungiyoyin Kwadago na kasar nan sun yi wa gwamnati barazanar cewa idan ba a saisaita musu mafi kankantar albashin da ake ta sa-toka-sa-katsin karawa ba, to za su yi amfani da kuri’un su a zaben 2019 su taka wa duk wanda ya hana su karin albashin burki.

Kungiyoyin Ma’aikatan sun yi wannan barazanar ce yau a bukukuwan Ranar Ma’aikata, wato 1 Ga Mayu da ake yi a kowace shekara daidai wannan ranar.

Ma’aikatan dai na so a kara musu albashi zuwa N65,000 a matsayin shi ne albashi mafi kankanta, a maimakon naira 18,000 da suke karba a matsayin mafi kankantar albashi a yanzu.

Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa Ayuba Wabba ne ya yi wannan barazanar yau Talata a Abuja, yayin da ya ke aikawa da sakon sa ga daukacin ma’aikatan Najeriya.

Ya ci gaba da cewa su fa yanzu tura-ta-kai-bango, sadoda haka a shirye su ke su yi taho-mu-gamu da gwamnati ko da masana’antu masu zaman kan su idan ba a kara albashi ba.

A ta bakin sa, ya ce kuri’un su su ne makaman su, kuma za su yi amfani da su wajen yaki da duk wanda ya yi musu kafar-ungulu daga biya musu bukatun su na karin albashi.

Share.

game da Author