Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Filato Kuden Kamshak ya bayyana cewa ana zaton wani ya kamu da cutar kurajen ‘Monkey Pox’ a jihar.
Kamshai ya sanar da haka wa manema labarai a garin Jos inda ya kara da cewa mutumin da ake zaton ya kamu da cutar na samun kula a kebabben wuri a asibitin koyarwa na jami’ar Bingham dake jihar.
” Mu na jiran sakamakon gwajin jinin wannan mutumi da muka aika Abuja domin samun tabbacin cutar da yake dauke da ita.”
Ya kuma yi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankalin su saboda gwamnati ta yi tanadin hana yaduwar cutar.
Idan ba a manta ba a 2017 cutar kurajen ‘Monkey Pox’ ta bullo a jihohi 23 a kasar nan wanda a dalilin haka mutane da dama suka rasa rayukan su.
Jihohin da suka yi fama da wannan cutar sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kaduna, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Lagos, Ondo, Oyo, Nasarawa, Niger, Rivers da Abuja.