Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya karyata labaran da wasu ke yadawa a soshoyal midiya cewa ya kai ziyara ga Sanata Jonah Jang, a kurkukun Jos, jihar Filato.
Ana tuhumar Jang da almubazzaranci da kudade a lokacin da ya ke mulkin jihar Filato.
Ofishin yada labaran Atiku ne ya karyata abin da ya kira jita-jita. Kuma ya ce Atiku bai kai ziyarar ba ballanatana har a ce ya raba makudan kudade kamar yadda ake yadawa.
Sanarwar ta kara da cewa a ranar da aka ce ya kai ziyarar, Atiku ya na Yola, kuma kowa ya tabbatar da haka.
Ta ci gaba da cewa tun a ranar Alhamis 17 Ga Mayu Atiku ke cikin Yola, kuma har yau ya na can.