Gwamnatin Jihar Kano ta bada hutu ranar Juma’a domin ta kasance ranar da za a yi wa gawar marigayi Sheikh Isyaka Rabi’u Sallah.
Babban malami, attajiri kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Khalifah Isyaka Rabiu ya rasu a Landan ranar Talata, bayan ya sha fama da jiyya.
Ya na rasu ya na da shekaru 93 a duniya.
Wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Mohammed Garba ya sa wa hannu, ta ce gwamnati ta dauke wa kowa zuwa aiki ranar Juma’a, domin musulmai su samu sukunin halartar jana’idar shehin malamin.
Za a yi masa Sallah ranar Juma’a, a masallacin Sheikh Isyaka Rabi’u da ke gidan sa a Goron Dutse, Kano, da misalin karfe 2:30 bayan kammala Sallar Juma’a.
Wata sanarwa daga hannun iyalan sa, ta bayyana cewa ya rasu ya bar ‘ya’ya 42, cikin su har da babban dan sa Nafi’u Rabi’u, sai shugaban kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabi’u, da shugaban kamfaninn jirajen 1RS, Rabi’u Rabi’u.