Jam’iyyar APC Akida da na Restoration a jihar Kaduna sun bayyana cewa a halin da jam’iyyar APC ta shiga a jihar na rashin zaman lafiya da nuna wariya da mulkin kama karya da ake yi wa ‘ya’yan jam’iyyar, za su kare ne kawai su fice daga jam’iyyar, ya fi musu zaman lafiya tun suna da kima a idanuwar jama’ar jihar.
Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Shehu Sani na daga cikin jiga-jigan yan jam’iyyar da basa ga maciji da jam’iyyar a jiha da fadar gwamnatin Jihar.
Wasu daga cikin mambobin wannan bangare na jam’iyya da ke adawa da jam’iyyar a jihar sun hada da Honarabul Isah Ashiru Kudan, da yayi takarar fidda dan takarar jam’iyyar da gwamna mai ci a 2015.
Shugaban kungiyar APC Akida, Mataimaki Tom Mai Yashi, ya bayyana cewa irin wariya da watangarerewa da jam’iyyar ke yi a jihar saboda mulkin kama karya da akeyi a cikinta ya sa dole mu dauki wata hanyar.
” Kaf yanzu a jihar Kaduna talakawa sun sire da wannan mulki na APC a jihar. Duk ko ina ba dadi. Ana taka talakawa gaba gadi babu tausayi, bayan ba abinda muka yi musu alkawari ba kenan.
” Baya ga haka an yi amfani da karfin mulki wajen nada shugabannin jam’iyya da ba zabin jama’a bane a fadin jihar.”
A dalilin haka ne wadannan bangarori na jam’iyyar APC a jihar, suka yanke shawarar zasu nemi wata jam’iyyar su koma.
Jam’iyyar APC a jihar ta shiga halin kakanikayi tun bayan raba jiha da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar suka yi watanni kadan baya ta kafa gwamnati a jihar.
Sanata Shehu Sani ne suka fara saka kafar wando daya da gwamnan jihar Nasiru El-Rufai, sun yi takai ruwa rana a tsakanin su saboda rashin amincewa da yadda gwamnan El-Rufai ya dauko salon mulki a jihar.
Daga baya kuma, rumui-rumui, suna dasawa da sanata Sule Hunkuyi sai aka rikito, soyayyar ta zama kiyyaya, aka fara rushe-rushen da zage-zage in da har gwamna El-Rufai ya tsitsine masu gaba daya saboda kin amincewa da saka masa hannu ya karbi bashi daga bankin duniya.
Yanzu dai kusan ta ko ina ana zaman doya da manja ne a jihar tsakanin bangarorin magoya bayan jam’iyyar.
A haka dai kowa ya wasa wukarsa yana jiran a buga gangar siyasa.