Isra’ila ta kashe Falasdinawa 41

0

Akalla an kashe Falasdinawa 41, kuma dubbai sun ji raunuka yayin da hargitsi ya barke kusa da kan iyakar Gaza da Isra’ila.

Wadanda suka rasa rayukan na su a yau Litinin sun yi kokarin tsallakawa ne cikin Isra’ila, kamar yadda jaridar Israel Daily ta tabbatar.

Zanga-zangar kin amincewa da bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Jerusalem ta yi muni a yau ranar da aka bude ofishin jakadancin na Amurka a Jerusalem.

A lokacin da ake hargitsin surikin Trump da ‘yar sa Ivanka su na wurin bikin bude ofishin.

An ruwaito cewa jami’an tsaron Isra’ila sun yi amfani da bakonon tsuhuwa da harsasai wajen hana Falasdinawa tsallakawa.

An kuma tabbatar da cewa an kashe kananan yara kuma wasu yaran sun ji ciwo a wurin.

Share.

game da Author