Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa hukumar ba ta da wani rakod mai nuna cewa kananan yaran da aka nuna sun a dangwala kuri’a a Kano na da rajista da INEC.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya yi wannan jawabi a wani taro da manema labarai a yau Juma’a a hedikwatar hukumar a Abuja.
An dai nuno yaran ne sun a dangwala kuri’u a zaben kananan hukumomi na jihar Kano, da hukumar zaben jihar ta shirya kuma ta gudanar.
Zaben kananan hukumomi dai hukumar zabe ta jiha ce ke shirya shi, kuma karkashin gwamnatin jiha ta ke, ba a karkashin INEC ba.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya yi wannan jawabi a wani taro da manema labarai a yau Juma’a a hedikwatar hukumar a Abuja.