HARIN MUBI: Atiku ya Kai tallafi

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya tallafawa mutanen karamar hukumar Mubi da suka fada tsautsayin harin Boko Haram da naira miliyan 10.

Atiku ya danka wannan kudi ne a wata asusu na tallafi dake karkashin ikon asibitin gwamnatin tarayya dake Yola mai suna (Yola’s Paupers Funds’) domin taimaka wadanda ke kwance a asibitin.

Idan ba a manta ba a ranar Talatar makon jiya ne wasu mahara wanda ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka tada bama bamai a masallaci da cikin kasuwar ‘yan gwanjo dake Mubi inda mutane 69 suka rasa rayukansu sannan da dama suka sami rauni.

‘‘Zuciyata ta karaya matuka a lokacin da naga halin da wadannan mutane ke ciki a asibiti. Sannan ina Kira ga gwamnati da ta karkato akalar ta zuwa ga ganin tsaro ya wadata a kasar nan.”

A karshe shugaban asibitin Auwal Abubakar ya mika godiyarsa a madadin marasa lafiyan ga tsohon mataimakin shugaban kasa sannan ya tabbatar masa cewa za su yi amfani da wadannan kudade yadda ya Kamata.

Share.

game da Author