GANIN LIKITA: Buhari zai tashi zuwa Landan Yau

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tashi zuwa kasar Britaniya don ganin ganin likitocin sa a yau Talata.

Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ne ya sanar da haka a wata takarda da ya saka wa hannu.

Shehu ya ce shugaba Buhari zai yi kwanaki hudu a kasar Britaniya inda ake sa ran zai dawo ranar Asabar, sannan kuma ya karkata zuwa jihar Jigawa domin yin ziyarar aiki na kwanaki biyu.

Share.

game da Author