Duk da kashe-kashe, kone-kone da rotse-rotse da aka yi, jam’iyyar APC ta ce an yi zaben shugabannin mazabu ‘lami lafiya’

0

A bisa dukkan alamu dai jam’iyyar APC ta zama gwano, wadda ba ta jin warin jikin ta, sai dai warin jikin wasu.

Duk da rahotannin da kafofin yada labarai na jaridu, talbijin, radiyo har ma da shafukan soshiyal midiya su ka nunawa, cewa an yi kashe-kashe, kone-kone da kuma ji wa da dama rotse, sai ga shi jam’iyyar APC ta bayyana cewa an kammala zaben lami lafiya.

Kakakin jam’iyyar Bolaji Abudullahi ne ya bayyana haka tare da taya wadanda suka yi nasara tare da jam’iyyar murna.

Sai dai ya ce duk da cewa an dan samu rashin jituwa a wasu wurare ko wasu jihohi, to zaben ya wanye lami lafiya.

Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito yadda aka samu asarar rayuka, fadace-fadace, buge-buge da jefe-jefe, har ma da inda wasu manya na kasar nan su ka rika yi wa junan su zagin-kare-dangi.

Cikin wasu jihohi da PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo rahoto, sun hada da: Bauchi, Delta, Ebonyi, Enugu, Oyo, Abia, Imo da Rivers.

PREMIUM TIMES HAUSA ta kuma gano cewa a wasu jihohin tilas ko kuma wasu dalilai sun sa ba a gudanar da taron ba.

A jihar Delta an burma wa wani dan takarar shugabancin karamar hukumar Ughelli wuka, kuma nan take ya mutu, aka bar shi kwance a cikin jini. Jemerier Oghaweta ya gamu da ajalin sa ne a mazabar Jeremi Ward 3, da ke Okwabe.

A jihar Ekiti kuwa an samu rahoton afkuwar buge-buge har da rotshe a kawunan mahalarta tarukan a mazabu da dama. Wannan ya sa tilas aka dakatar da taron gangamin zaben.

Can a jihar Rivers kuwa Ministan Sufuri Rotimi Ameachi da Sanata Magnus Abeh, sun kwashi ‘yan kallo, yayin da suka rika surfa wa juna bakaken kalamai marasa dajin ji. Ameachi ya zargi Abbe da cewa ya nemi yin karfa-karfar dora shugabanni ba tare da yin takara ba.

A jihar Ebonyi kuwa, da ya ke can jam’iyyar APC ta rabu gida biyu, kowane bangare ya gudanar da na sa zaben can daban.

Ministan Harkokin Waje kuwa bai ji dadin yadda aka gudanar da zaben a jihar sa ta Enugu ba, dalili kenan ya yi wa zaben tofin Allah-tsine.

Da ya ke ganawa da magoya bayan sa, Minista Geoffrey Onyeama ya yi kuman cewa a yayin taron, gaba dayan jihar an maida shi da mutanen sa saniyar-ware.

Rahotanni sun nuna cewa a jihar Bauchi kuwa har ofishin jam’iyya na karamar hukumar Ningi aka banka wa wuta, saboda zargin yin magudi can a tsakanin su ‘ya’yan jam’iyyar APC.

Share.

game da Author