Dubban jama’a ne suka taru a Maiduguri, babban birnin jihar Barno, inda suka yi wa tsohon gwamnan jihar, Ali Madu Sheriff lale marhabin da komawa cikin jam’iyyar sa ta ainihi, APC
Sanata Sheriff dai a baya ya tuma tsalle ya koma jam’iyyar PDP, inda har ya yi shugabancin jam’iyyar.
Bayan rikicin shugabanci ya harde, har zuwa Kotun Daukaka Kara, Sheriff ya koma APC kwanan nan bayan an yi ta yada rade-radin cewa ya koma, amma jam’iyya mai mulki ta na karyatawa.
Ya fice daga APC ne a cikin 2014, bayan da rikici ya harke tsakanin sa da yaron sa, gwamna na yanzu, Kashim Shettima da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar na kasa baki daya.
A lokacin da Sheriff ya koma jam’iyyar PDP, da yawan magoya bayan jam’iyyar APC, har ma da manyan, sun rika bin sa da jifar munanan kalamai, su na alakanta shi da Boko Haram.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa tun da Sheriff ya fice daga gidan gwamnatin jihar Barno, har yau bai kara shiga ciki ba, saboda sabanin da ke tsakanin sa da gwamna Shettima.
Cikin wadanda suka yi jawabai a wurin taron, har da Gwamna Kashim Shettima, wanda yay i bayani sosai, kuma ya ce za a guji dora duk wani dan takarar da ba shi jama’a ke so ba a dukkan mukaman da za a yi takara a siyasa.
Shi ma Sanata Ndume da Kashim Imam, sun nuna farin cikin su, kuma sun nanata cewa daga yau duk wata adawa, gaba ko sabani ya kare.
A na sa bangaren, kowa ya yi tsammani Sanata Sheriff zai tashi ya yi bammabmi, amma sai ya nuna dattako, inda ya yi kira a samu hadin kai domin a kara ciyar da jihar Barno gaba.
Daga cikin magoya bayan PDP kuwa, da dama su na murna da ficewar Sanata Sheriff daga jam’iyyar, domin ko ba komai, kamar yadda wasu kec cewa, za su ga wani maras kunyar da zai rika cewa PDP ta rungumi dan Boko Haram cikinn jam’iyyar ta.
A cewar su, dama can Sheriff dan APC, kuma ko dan wa ne ma dai, dan su ne.
Abin tambaya a nan shi ne, ko magoya bayan APC za su rika cewa Buharin ya rungumi dan Boko Haram shi ma?