Daraktan NYSC, Kazaure ya hori ‘yan bautar kasa su kiyaye karya dokokin zabe

0

An hori masu bautar kasa na wannan zubin da su kiyayi duk wasu laifukan da su ka danganci cuwa-cuwar karya dokokin Hukumar Zabe, INEC a duk inda aka tura su gudanar da ayyukan zabe.

Babban Daraktan NYSC na kasa ne, Sulaiman Kazaure ya bayyana haka, a cikin wata takarda da jami’in hulda da ‘yan jaridu na hukumar, Adenike Adeyemi ya sa wa hannu, a yau Alhamis.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban na NYSC, Sulaiman Kazaure, ya yi bayanin ne a sansanin masu bautar kasa na Iyana-Ipaja da ke Lagos, yayin ziyarar da ya kai wurin bikin faretin kammala horo na Zubi na 2018 ‘A’.

Ya ce doka za ta hau kan ko ma wa aka kama ya aikata ba daidai ba a yayin gudanar da ayyukan zaben kasar nan.

Kazaure ya ce hukumar NYSC ba za ta zura ido wasu tsiraru su bata mata suna da kimar da ta shafe shekara da shekaru ta na gina wa kan ta ba.

Ya ce daya daga cikin abin da ke gaban hukumar shi ne kara tabbatar da jin dadi, kare lafiya da dukiyoyin masu bautar kasa.

Shi ma gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode, ya yi musu irin gargadin da shugaban hukumar ya yi musu, tare da cewa jihar Lagos za ci gaba da tallafa musu kamar yadda ta saba.

Share.

game da Author