Sufeto janar na ‘Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bayyana cewa bai karya dokar kasa ba kin amsa gayyatar majalisa da yayi.
Idan ba a manta ba majalisar dattawa ta bukaci Ibrahim Idris da ya bayyana a gabanta domin yi mata bayani kan dalilan da ya sa ake ci gaba da tsare sanata Dino Melaye, sannan kuma yayi bayani kan yanayin tsaron kasa.
Sau uku suna gayyatar sa amma bai samu daman zuwa zauren majalisar ba har yanzu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan kasa, Moshood Jimoh, ya fadi a wata takarda da Sufeto janar din ya sa wa hannu cewa dokar kasa ta ba shi damar zai iya aikawa da wasu jami’an ‘yan sanda a madadin sa domin su wakilce shi amma majalisar taki amincewa da haka.
Ibrahim Idris ya ce ya sani majalisar na shirya masa kutunguila ce da idan ya bayyana a majalisar sai su wulakantashi, su ci masa mutunci sannan su tozarta shi.
Ya ce abinda ya sa kenan ya ke bayyana a gaban majalisar.
Majalisar dattawa dai a zamanta na yau ta ce ta bar sufeto janar din da halin sa kuma da dimokradiyya cewa ya je ya gani.