Dalilin da ya sa na ke neman hukuncin kisa kan masu yada kalaman kiyayya – Sanata Sabi

0

Sanata Sabi Abdullahi, wanda ya gabatar da kudirin neman hukuncin kisa kan masu yada kalaman kiyayya, ya bayyana dalilan san a yin haka.

Ya ce ya yi haka ne ba don ya ingiza a kakaba wa kafafen yada labarai takunkumi ba, ko a dakile ‘yancin fadar albarkacin bakin ‘yan Najeriya.

Sanata Sabi, dan jam’iyyar APC mai wakiltar Jihar Neja shiyyar Arewa, yayi karin hasken cewa idan har aka kafa dokar, to ‘yan Najeriya za su shiga taitayin su, ta yadda za a kara samun dankon zumunci tsakanin yankunan kasar nan da junan su.

Ya ci gaba da cewa kafa dokar zai kawar da yadda ake yawan dibga kasassaba, katobara, izgilanci da muzanta juna da munanan kalaman da ke iya haddasa mummunan rikici da kashe-kashe maras dalili.

Sanatan ya yi wannan jawabi ne a wani taro na Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida na Duniya. Na sheakarar 2018 da Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya.

Ya kara nuna cewa yawan yayata kalaman kiyayya a kasar nan, musamman a wasu kafafen yada labarai na soshiyal midiya, abin firgici da kuma tashin hankali ne matuka.

Ya ce idan ba a yi wa tubkar hanci ba, to ya na gudun kada wata rana irin wadannan kalamai su haddasa rikice-rikice, alhali Najeriya babu abin da ta ke bukata kamar zaman lafiya da ingantuwar zamantakewa tsakanin mazauna sassan kasar nan daban-daban.

Abdullahi shi ne Shugaban Kwamitin Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Majalisar Dattawa.

Share.

game da Author