Sanata Dino Melaye ya diro ne daga cikin motar ‘yan sanda saboda daya daga cikin su ya fesa masa barkonon-tsohuwa a idanu da hanci ne a cikin motar.”
Sanata Murray Ben-Bruce ne ya furta haka, ranar litinin bayan ya kai wa Dino ziyara asibiti, ya na mai cewa ba ya farin ciki da irin hali da yanayin da ya samu Dino a ciki.
“Na je na gano Dino a asibiti. Ban ji dadin yadda na same shi ba. Dino ya na fama ciwon asma, amma a kan hanyar su a ranar da aka dauko shi, wani dan sanda ya fesa masa barkonon-tsuhuwa a ido, har ta kai numfashi ma ya kusa ya gagare shi.
“Wannan ne dalilin da ya sa ya yi wuf, ya fito daga cikin motar. Maganar gaskiya ita ce, Allah dai ya sa ya na da sauran kwana a gaba, amma kadan ya rage ya mutu a lokacin.” Inji Sanata Bruce.
Kakakin ‘yan sandan Abuja Jimoh Mosheed bai amsa wayar da aka buga masa domin a ji ta bakin sa dangane da wannan zargi da aka yi wa ‘yan sanda ba.