Dalilin da ya sa Buhari ya yada zango a Landan -Fadar Shugaban Kasa

0

Mai Magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya bayyana dalilin da ya shugaban ya yada zango Landan bayan tasowar sa daga Amurka ranar Talata.

Ya ce wasu dalilai ne masu karfi suka sa aka yada zango Landan, maimakon ya zarce kai tsaye zuwa Abuja daga birnin Washington na Amurka.

Shehu ya maida wa PREMIUM TIMES wannan martanin ne, bayan da wannan jarida a yau da rana ta buga labarin cewa kwana biyu kenan tun bayan da Buhari ya baro Amurka, amma babu labari.

Ya ci gaba da cewa babban jirgin shugaban kasa ne ake gyara, shi ne suka ajiye shi suka tafi da karamin jirgi.

“Ana gyara babban jirgin Shugaban Kasa ne. Shi kuwa karamin jirgi ya na da iyar adadin nisan zangon da ba a so ya wuce.”

“Maganar da na ke nufi a nan ita ce, an tsaya ne a yi wa jirgin sabis, idan aka gama, ya sha mai kuma sai ya dauko hanya zuwa Abuja. Wato a takaice an raba tafiyar biyu kenan.

Ya ci gaba da cewa wannan duk ba wani abu sabo ba ne, duk cikin harkokin tafiye-tafiye ne.

A lokacin ya ce har ma Buhari ya kamo hanya zuwa Abuja.

Ya kara da cewa daga Abuja zuwa Washington tafiyar awa 12 ce, shi kuma wannan karamin jirgin, awa sha biyu da minti 40 cif ita ce iyar adadin tafiyar da ake so ya yi a rana daya. Kun ga dalilin da ya sa ba a so a takura wa jirgin kenan, tunda karami ne.”

Share.

game da Author