Dalibin jami’a ya saci motar makwabta, ya bugar da ita N120,000

0

An gurfanar da wani dalibin jami’a mai suna Opemiposi Okunuga, a kotu bisa tuhumar shi da zargin ya saci motar makwauci, kuma ya saida ta a kan kudi naira 120,000.

Okunuga, mai shekaru 21 da haihuwa, an gurfanar da shi ne a Kotun Majistare ta Ikeja, Lagos a yau Alhamis.

Mai gabatar da kara Godwin Awase, ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya tabka satar ne a ranar 1 Ga Mayu, 2018.

Ya saci motar wanda ya kawo shi kara ne mai suna Ola Oladipopu.

Ya ce bayan ya ajiye motar a gaban gidan sa, sai wanda ake zargin ya yi wa motar janwai ya kai ta wata mabuya.

Motar wadda kirar Mazda ce, Ola ya ce bayan ya fito bai ga motar sa ba, sai ya fara kuwwa ya na raki. Nan take sai wani makwauci ya ce ai kuwa sun ga wanda ake zargin su a jan motar sun fice da ita.

Bayan ya kai kara ne, ‘yan sanda suka je suka kamo wanda ake zargin.

Dan sanda mai gabatar da kara, Awase, ya shaida wa mai shari’a cewa wanda ake zargin yace ya sayar da motar naira 120,000 kacal ne.

Sai dai kuma da aka je bagan alkali, dalibin yace atafau bai saci motar ba.

Duk kokarin da suka yi domin su gano wanda ya sayi motar, ya ci tura.

An daga shari’ar zuwa ranar 23 Ga Mayu, 2018.

Sai dai kuma an bada belin sa a kan naira 200,000 tare da mutane biyu da za su iya tsaya masa.

Mutanen biyu kamar yadda mai shari’a ya ce, su kasance su na da rasidan shaidar biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas har na shekara biyu-biyu kowanen su.

Share.

game da Author