Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma na kasa (NANNM) ta yi kira ga gwamnati da ta daidaita albashin duk ma’aikatan jinya dake aiki a kasar nan. Cewa hakan ya zama dole don inganta ayyukan ma’aiakatan da samun natsuwa.
Shugaban kungiyar Margaret Akinsola ce ta yi wannan kira sannan ta bayyana cewa bambanta albashin ma’aikatan jinyan dake aiki da asibitocin kasarnan ne ya sa ake samun rarrabuwar kai da ki da wasu ke yi na su yi aiki a kananan hukumomi ko kauyuka.
” Idan gwamnati ta kawar da wannan bambanci na albashin ma’aikatan jinya za su yarda suna aiki a asibitocin dake kauyuka ganin cewa nan aka fi bukatar su.
Discussion about this post