Hansatu Mustapha, mace ce mai shekaru 36, ta kasance ba ta da wani zabi sai matawa da garin su Konduga, garin da Boko Haram su ka fatattaka, gaba daya al’ummar garin suka fashe zuwa cikin Maiduguri, kamar shekaru uku da suka gabata.
Matar mai ‘ya’ya takwas, ta na cikin ‘yan kalilan da suka samu kubuta gaba dayan su. Domin ba ta rasa ‘ya’ayan ta ko guda daya ba, sai dai kuma ta yi asarar komai a garin Kodunga.
“Mu na cikin zaman jin dadi da kwanciyar hankali da miji na da ‘y’ayn mu a Konduga, kusan shekara 20 da yin aure, sai Boko Haram su ka kai mana mummanan hari. To a nan ne na tabbatar da rudin kai na da nake yi, na ce ashe dai mafarkin da na ke cewa Konduga ta fi ko’ina dadin zama a duniya, duk mafarki ne, ba gaskiya ba ne.
“A halin yanzu ba ni da komai, ba ni da kowa sai yara na da na ke kula da su.”
“Kwata-kwata garin Konduga, inda can ne mahaifa ta, ya fita daga raina gaba daya. Garin da Boko Haram suka kashe min miji na aka bar ni da marayu, me zan yi da shi, ga shi kuma ba ni da sauran komai a ciki.
Garin Konduga dai ya sha fama da hare-haren Boko Haram, amma ba su yin nasar saboda tashi-tsayen da sojoji suka rika yi a lokacin su na hana su kutsawa. Amma a ranar da suka yi galabar shiga garin, a ranar kowa ya ji a jikinn sa. A ranar da suka an yi bata-kashi sosai.
A cikin garin Kwanduga ne a watan Satumba, 2014 sojoji suka ce sun kashe Abubakar Shekau. Amma daga baya aka gano cewa ba gaskiya ba ne, wani dai ne aka kashe mai kama da shi.
Da Boko Haram sun yi nasarar karbe Konduga a lokacin da su ke zabari da kumajin kai hare-hare barkatai, to kuwa da sun samu saukin kai wa Maiduguri mummunan hari, ko kuma su kwace Jami’ar Maiduguri, wadda ke wajen gari, kan hanyar zuwa Bama.
Amma lokacin da Boko Haram suka samu gabalar shiga Konduga, a lokacin karfin su ya ragu sosai, ba su da namijin kusarin tunkarar Maiduguri, kuma daidai lokacin an damfare sojoji jingim a babban birnin na jihar Barno.
A yayin harin da suka kai wa Konduga, wanda yay i sanadiyyar al’ummar ganin fashewa kowa ya tsere, Hansatu ta ce mijin ta ya ji mummunan rauni, amma yay i ta-maza shi ma ya gudu daga garin, duk kuwa da irin mummunan halin da ya ke ciki.
“Kafin mu kawo kan mu Maiduguri, sai da muka shafe kwanaki uku mu na ta walagigi a cikin daji. Da muka zo, to mun yi sa’a Bulama na Modusulumri ya san miji na. Sai ya ba mu daki daya, inda ni da miji na da ‘ya’yan mu takwas mu ke kwanciya a ciki.’’
RAYUWAR HANSATU BAYAN BA MIJI
Hansatu ta kasance ita ce maigida-kan-gidan ta, domin mummunan ciwon da mijin ta ya ji sanadiyyar harbin bindiga da aka yi masa shi ne sanadiyyar ajalin sa.
“Duk da ciwon da miji na ya ji daga harbin da Boko Haram su ka yi masa, haka ya yi ta gaganiya na fadi-tashin ciyar da mu, har ajalin sa bayan shekara uku da harbi. Daga nan fa ne duniya ta yi min kunci da duhu, saboda an bar ni da nauyin yara takwas a gaba na.
“Tsayawa ma ina bada labarin irin wahalar da mu ka shiga, shi kan sa wata wahalar ce mai zaman kan ta.
Ta ci gaba da cewa su da a can baya su ke rayuwa cikin rufin asiri da wadata, sai ga shi sun koma rayuwar kaskanci, wulakanci ta katutun fakirancin da abinci ma ba ka san lokacin da za ka gani ba, balle a ba ka har ka ci.
“A haka muka rika rayuwa a cikin dogaro da dan abin da makwauta za su ba mu mu ci, wadanda su din ma mabukata ne, ba wadatar gare su ba, domin idan aka ba su dan abin da suke ba mu, su ma karba za su yi.” Inji Hansatu.
“Haka na rika fita kwararo-kwararo, gida-gida ina neman aikatau; a matsayi nan a uwa da ke da yara takwas a gaban ta, cikin su har da matasan ‘yan mata, na hana ‘yan matan cikin su fita waje neman aiki, don gudun kada a bata su. Saboda na ga irin yadda maza marasa imani ke amfani da talaucin mata ‘yan gudun hijira sun a bas u dan abin duniya kalilan sun a lalata da su don su samu na sayen abinci. Wasu kuma su ciyar da iyalin su.
“Duk ranar da na fita ina aikatau a gidaje kamar wankin kayan matar gida da na yaran ta kanana da wanke-wanke, na sha fama da musgunawa da cin zarafi, amma sai na danne zuciya ta, saboda na fita ne neman abin da iyali na za su ci.
MAHAKURCI MAWADACI
“Ba mu samun sukunin rayuwa ba sai da shekara uku cur ina gaganiya a cikin kaskanci, sai wata rana wata kungiyar bayar da tallafi ta kasar Norway, (Norwegian Refugee Council), su ka zo unguwar mu sun a daukar wadanda za su yi wa horon koyon sana’o’i.
“Ni da wasu mata aka koya mana yadda za mu yi kananan sana’o’I, kuma aka ba kowanen mu N43,500 kyauta domin mu ja jarin yin sana’ar duk da nag a zan iya yi.” Inji Hansatu.
Dalilin wannan ne yanzu Hansatu ta samu sukuni, ta daina fita yawon nema, ta kama sana’a kuma ta na samun nasibi. Ta ce yanzu dukkan yaran ta sun a zuwa makaranta, kuma jari da na kara habbaka.
NI DA KONDUGA HAR ABADA
Cikin watan da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Barno ta yi shelar maida ‘yan gudun hijirar Bama zuwa gida domin ana kan aikin sake gina garin da gwamnatin jiha da ta tarayya key i.
Garin Konduga ya na kilomita 37 tsakanin sa da Bama, daga Maiduguri. Wato kenan tunda jama’ar Bama za su iya komawa gida, su ma na Konduga kenan za su iya komawa.
Akwai mutane kalilan a yanzu da ke zaune a sansanin Konduga. Amma dai akasarin mutanen garin duk sun fashe.
Amma wannan labarin komawa gida, sam bai faranta wa Hansatu rai ba, cewa ta yi ma it aba za ta koma ba.
“Na sha azaba, na rasa komai a garin. Me zan koma kuma na yi a Konduga. Ni fa ko mafarkin komawa garin nan ban a fatan na kara yi, sannan ko tuna garinn nay i sai fargaba ya kama ni. Me zan koma na yi a garin da ba ni da kowa, ba ni da komai?
“Dan uwan da kawai na ke da shi a Konduga, shi ne miji na, kuma yam utu. Shin idan ma na ce zan koma, to a gidan wa zan zauna? Ni yanzu na yanke shawarar rayuwa a cikin Maiduguri, inda a nan na fi jin cewa rayuwa ta ba ta tattare da wata barazana. Kuma b azan sake yin fatar sake jefa yara na cikinn wani garari ba.
“Masu cewa na koma ai bas u san irin wahalar da muka sha a daji har kwanaki uku kafin mu kawo kan mu Maiduguri daga Konduga ba.
Hansatu ta ce akwai wadanda su ka fi ta shan azaba sosai, wadanda har yanzu babu mai taimaka musu.
“Amma mu a nan unguwar Modusulumri an ba mata 200 kowace naira 43,500 kyauta, domin yin kananan sana’o’i. amma har yanzu akwai wadanda ke fama da rayuwar kunci.”
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa akwai sama da ‘yan guun hijirar Boko Haram da ke cikin Maiduguri da kuma cikin sansanonin ‘yan gudun hijira.sai dai rahoton ya kara da cewa, mutane 230,000 ne kadai ke zaune a sansanoni daban-daban.
Sauran kuma kamar yadda rahoton ya nuna, duk sun a cikin gari a gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki. Kena kimanin miliyan 2.7 ne warwatse a cikin jama’a.