Bankin CBN ya kara zuba dala miliyan 100 domin maniyyata su samu saukin canjin kudade

0

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya zuba dala milyan 100 a kasuwar hada-hadar canji, kwanaki daya bayan ya saki dala milyan 210 domin maniyyata su samu saukin yin canjin kudade.

Haka CBN ya bayyana a cikin wani jawabi da bankin ya aika wa PREMIUM TIMES, cewa an antaya milyoyin dalolin a kasuwa ne domin kauce wa amfani da wannan lokaci a har wasu su shake wuyan kasuwar hada-hadar canjin kudade a samu cikas.

Ya ci gaba da cewa hakan zai saukaka wa dukkan maniyyaci ya samu damar canjin kudi a saukake.

A ranar Laraba ne dai CBN ya fara antaya dala milyan 210 domin hada-hadar canjin kudaden maniyyata, sannan jiya Alhamis ya kara sheka wasu dala milyan 100.

Kakakin yada labarai na CBN, Isaac Okorofor, ya ce nan da wasu ‘yan kwanaki kadan za a kara antaya wasu milyoyin dalolin domin kauce wa duk wata hanya da wasu za su bi su tsawwala farashin dala ko kuma su haddasa karancin ta.

Ganin yadda aikin Hajji ya yi tsada daga shekarar da ta gabata zuwa 2018, har yau da yawan maniyyata ba su kammala biyan kudaden tafiya ba.

A shekarar 2016 dai naira 850,000 ana biya karamin tikiti, amma da 2017 da 2018 yanzu karamin tikiti ya kai miliyan daya da rabi, kadan ne babu.

Share.

game da Author