Akwai ragowar masu halayyar Malam Aminu Kano a Arewa kuwa? Daga Mustapha Soron Dinki

0

Malam Aminu Kano ya rasu a 1983,lokacin da wasu daga cikinmu ba’a haifesu ba.

Tarihi ya nuna mana shine mutumin daya fara gwawarmayar fitar da talakawa daga mulkin kama-karya na shugabanni da attajirai na wancen lokacin wanda turanci ake kiransa da ‘Semi-feudal dominance’.

Aminu Kano yayi shuhura wajen gwagwarmaya wacce take da siffa irinta ‘Karl Marx’ amma sun bambanta domin shi Malam Aminu bai saki al’adarsa ba kuma bai yi fada da addini ba irin yadda ‘Marx’ yayi.

A ilimance, duk mutumin da zai jagoranci talakawa wajen samar musu da ‘yancin fadar ra’ayinsu da fitar dasu daga Kangin mulukiya dole za’a kirashi da ‘socialist’ ko ‘Marxist’.

Son talakawa ne yasa ya kirkiro kungiya wacce ta zama jam’iyarsu daga baya. Talakawa da yawa a arewa sun samu damar zama manyan ‘yan boko, yan kasuwa da siyasa ta silarsa.

Allah ya hadamu dashi a aljanna. Tsakani da Allah, duba da wannan takaitaccen bayani da mukayi akan Malam Aminu Kano.

Wai kuwa akwai ragowar yaran sa a Arewa? Gaskiya akwai tunda gasu nan muna ganin su da irin shigarsa sai dai bana jin akwai wani babba a arewa da yake da kusanci da talakawa irin na Aminu Kano.

Rannan naji hirar Abdulmajid Danbilki Kwamanda a Aminci radio yana cewa “Wallahi da Buhari ya bude kofar karbar shawarar manyan Arewa ba zai yiwa talakawa aiki ba saboda wai basa son cigaban talaka” Gaskiya duk da wasu suna gani kamar cin mutuncin mutane yake,a nan dai ya wurgawa kowa Kalubale, sai kowa ya duba dattijai, yan boko, yan kasuwa da yan siyasar da yake da alaKa dasu don ya tabbatar da gaskiya ko Karyar Danbilki.

Ni dai ban san mutum goma da suke da kusanci da talakawa ba, ban kuma ce babu ba.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author