A yau Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta fadi cewa ba a rasa rai ko daya ba a harin da aka kai kauyen Auno, jihar Barno.
Idan ba a manta ba jiya Laraba ne wasu jami’an tsaro da mazaunan kauyen suka bayyana wa PREMIUM TIMES cewa wasu mahara da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai musu hari.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun far wa kauyen ne da karfe takwas na yammacin Laraba inda kowa da kowa ya arce daga garin.
Sai dai jami’an tsaro na rundunar ‘yan sanda da na sojoji basu ce komai game da harin ba tun jiya sai yau Alhamis.
A karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Barno Edet Okon ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa wasu ‘yan Boko Haram ne suka kai wa shigen soji dake kauyen Auno hari da karfe bakwai na yammacin Laraba amma dakarun su sun fatattake su kafin su aiakata abin da suke so suyi.