Majalisar Jihar Kano ta dage zaman ta tun daga yau Litinin, 14 ga Mayu, har zuwa karshen watan Yuni.
Daraktan Yada Labaran Majalisar, Ali Bala ne ya sanar a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Ya ce an tafi hutun ne domin azumin watan Ramadan da kuma Karamar Sallah.
Tuni dai ‘yan sanda suka rufe majalisar, inda suka hana manema labarai shiga ciki.
Sai dai kuma wani ma’aikacin majalisar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an yi yunkurin tsige Kakakin Majalisa ne, Abdullahi Ata, domin har sai da babban dogarin majalisa ya je da sassafe da nufin ya boye sandar mulkin majalisa.
Rufe majalisar ya daidai lokacin da ake rade-radin shirin tsige kakakin majalisa, Abdullahi Ata, wanda ya canji tsigaggen kakakin, Kabiru Rurum.