An kawar Zazzabin Lassa a Najeriya – Ma’aikatar kiwon lafiya

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa an sami nasarar kawar da cutar Zazzabin Lassa a kasa Najeriya.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, sannan ya kara da cewa hakan ya yiwu ne bayan maida hankali da ma’aikatar sa tayi da kuma hadin guiwar kungiyar kiwon lafiya ta duniya da hukumar NCDC.

” Idan ba a manta ba tsakanin watannin Janairu zuwa Mayu na wannan shekara, Najeriya ta yi fama da wannan cutar fiye da na kowace shekara domin mutane 423 ne suka kamu da cutar sannan daga ciki mutane 106 sun rasu.”

Share.

game da Author