An kama gaggan ‘yan fashin bankin Offa da ake nema ruwa-jallo

0

Jami’an tsaro sun kama wasu gaggan ‘yan fashi biyu, daga cikin gungun wadanda suka yi mummunan kisa a fashin banki cikin garin Offa, a jihar Kwara.

An samu nasarar kama su makonni uku bayan an watsa hotunan su da kyamarar cikin banki ta dauki hotunan su a lokacin da suke bude wuta, sun a kashe mutane.

An dai yi asarar rayuka 17, ciki har da ‘yann sanda tara a fashin wanda aka yi ranar 5 Ga Afrilu, 2018.

Wadanda aka kama din sun hada da Kunle Ogunleye da aka fi sani da Arrow, mai shekara 35 da kuma Micheal Adikwu, dan asalin kabilar jihar Benuwe.

An kama Ogunleye a garin Oro, cikin jhar Kwara, yayin da shi kuma Micheal tsohon dan sanda ne, wanda aka kora cikin 012 bayan an kama shi da aikata mummunan laifi a lokaci.

An kama shi ne a lokacin da laifin cin amanar aikin dan sanda inda aka hada baki da shi ya kwance dan fashi da makami ya tsare.

Bugu da kari kuma, an tsare Micheal a gidan kurkuku, amma a can ma ya tsere a cikin 2015.

Share.

game da Author