A yau ne rundunar ‘yan sandar jihar Legas ta gurfanar da wani barawo da ya saci buhunan kwakwa 16 a kotun dake Badagry a jihar.
Dan sandan da ya shigar da karar Akpan Ikem ya bayyana a kotun cewa barawon kwakwan mai suna Demola Fadipe ya saci buhunan kwakwan ne ranar 9 ga watan Mayu a kasuwar siyar da kwakwa dake Agbalata, Badagry.
” Da ga aikan Demola da wadannan buhunan kwakwa ya kai wa wani kwastoma sai ya zarce da su gidan sa ya fara rabawa mutane da makwabta kyauta bin sa, ko me ya sa oho.”
” Mun damke Demola a lokacin da yake watanda da wannan kwakwa a unguwar da yake zama.”
A karshe Demola ya musanta aikata hakan amma alkalin kotun Jimoh Adefioye ya yanke hukunci ba Demola belin Naira 200,000 tare da takardun shaida biyu.
Za a ci gaba da sauraron karan ranar 18 ga watan Yuni.
Discussion about this post