Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan, ta bayyana cewa ta gano Babban Jami’in Diflomasiyyar Najeriya da aka kashe a Kahartum, babban birnin kasar.
An bayyana sunan sa Habibu Almu, kuma ma’aikacin Hukumar Shige-da-fice na a nan Najeriya, wanda aka tura aiki a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Sudan.
NAN ta ruwaito labarin kashe Almu, inda ta hakaito cewa a soshiyal midiya an ce an yi amfani da wuka wajen kashe shi a cikin gidan sa.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Sudan, ta nuna takaicin kashe shi da wasu suka yi, kuma ta ce gwamnatin Sudan ta na ta tsaurara bincike domin gano makasan.