Wasu likitoci a jami’ar gudanar da bincike dake Pokfulam kasar Hong Kong sun bayyana cewa sun gano maganin warkar da kanjamau mai suna ‘Bi-specific Broadly Neutralising Antibody (bNAb)’.
Likitocin sun furta haka ne bayan sun yi gwajin ingancin wannan maganin a jikin wasu beraye dake dauke da cutar. Gaba dayan su duk sun war ke ta-tas.
‘‘Berayen sun warke ta-tas daga cutar kanjamau gaba daya bayan da muka yi amfani da wannan maganin a jikin su’’.
A karshe likitocin sun ce kara inganta wannan maganin zai zama maganin kawar da ciwon kanjamau na farko da aka sarrafa a kasar Hong Kong sannan kuma zai taimaka wajen kawar da cutar a duniya.