An bai wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

0

Najeriya ta bai wa kamfanoni 13 lasisin gina kananan matatun mai. Kimanin kamfanoni 35 ne suka nemi a ba su lasisin, amma dai 13 ne kadai suka samu lasisin gina matatun.

Shugaban Hukumar NNPC na Kasa, Maikanti Baru ne ya bayyana haka, kamar yadda hukumar ta aika wa PREMIUM TIMES da bayani.

A cikin bayanin, Baru ya bayyana haka ne yayin walimar cin abinci a wani taron bayar da kyaututtuka da fannin harkokin man fetur da aka shirya a Amurka, inda a wurin ya zama bako mai jawabi, kuma har aka ba shi kyauta.

Ya ce kafa matatun na daya daga cikin kudirorin gwamnatin Muhammadu Buhari, domin shawo kan matsalar Neja Delta, inda a can ne ake hako man.

Ya ce gwamnati na fata kafa kananan masana’antun zai magance yawaitar satar danyen mai da ake yi a yankin na Neja-Delta.

Ya kara da cewa hakan kuma zai kara samar da ayyukan yi ga dimbin matasan Neja-Delta.

Baru ya ce kafa kamfanoni zai sauya Najeriya daga kasa mai fitar da danyen mai waje, zuwa kasa mai fitar da tataccen man fetur da sauran dangogin sa zuwa kasashen waje.

Ya kuma jaddada cewa Najeriya na kan kudirin ta na ganin ta daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje, nan da zuwa 2019.

Share.

game da Author