Akalla dalibai 120 ne a kowane aji a Jihar Katsina -Jami’in Ilmi

0

Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga a Ma’aikatar Ilmi ta Jihar Katsina, Kabir Ruma, ya bayyana cewa kididdigar da su ka gudanar ta kakar shekarar 2017/2018, ta nuna cewa akwai malamin makaranta daya tal ga kowane dalibin firamare 75 da ke jihar.

Ruma ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke gabatar da takarda dangane da matsayin karatun ‘ya’ya mata a jihar Katsina, a yayin nda babban jami’in kula da harkokin ilmin na Hukumar UNICEF ya kai ziyara Katsina.

Ya ce a karamar makarantar sakandare kuma akwai dalibai 68 ga kowane malami daya, babbar sakandare kuwa dalibai 46 ga kowane malami daya.

Kididdigar a ta bakin Ruma, ta tabbatar da yawan daliban firamare na jihar sun kai 1,604,423, na karamar sakandare sun kai 271,690, sai babbar sakandare kuma su 169,694.

Daraktan ya kara da cewa jihar Katsina na da malaman firamare 21,468, na karamar sakandare su 3,997 sai kuma 3,694 na babbar sakandare.

Akwai malaman da suka cancanci koyarwa sun kai kashi 72 a firamare, malaman karamar sakan dare da suka cancanci koyarwa sun kai kashi 81, su ma na babbar sakandare sun kaai kashi 81.

Sai dai Ruma ya yi bayanin cewa akalla akwai dalibai 120 a cikin kowane ajinn firamare daya, 75 cikinn ajin karamar sakandare, sain kuma 59 cikin kowane ajin babbar sakandare.

Share.

game da Author